News

Abba Kyari, Ta Hanyar Da Na Haɗu Da Hushpuppi Harma Na Yi Masa Dillancin Riguna Dama Huluna

Ta Hanyar Da Na Haɗu Da Hushpuppi Harma Na Yi Masa Dillancin Riguna Dama Huluna – Abba Kyari

“Asalin Sunansa Abbas Sai daga baya mu ka gano ana kiran sa Hushpuppi, ya kira ofishin mu kamar shekaru biyu da su ka gabata.

Sannan Ya Shugar Da ƙorafin cewa wani a dan Najeriya ya yi barazanar zai kashe shi da iyalan sa a nan Najeriya.

Sannan Kuma ya aiko mana Da lambar wayar mutumin, ya roƙi mu da mu gaggauta ɗaukar mataki tun kafin ya kai ga hallaka iyalan na sa.

“Sai Muka je muka gano inda wanda ake zargin ya ke, sannan mu ka yi bincike kuma mu ka gano gaskiyar magana babu wata barazanar kisa a lamarin.

Ashe ma abokan juna ne tsawon shekaru masu yawan Ggaske.Kawai dai akwai dan saɓani ne ya shiga tsakanin su a kan kuɗi.

Daga nan mu ka saki wanda ake zargin a kan beli. Ko kulle shi ma ba ayi ba.“Babu wanda ya nemi ko sisi a hannun Hushpuppi.

Mu a lokacin babban aikin mu shi ne mu hana wanda aka ce zai yi kisa aikata abin da aka ce mana zai aikata ɗin.

“To daga nan sai ya ga wasu hotuna da na ke sanye da kayan gargajiya a shafi na na soshiyal midiya. Ya ce ya na buƙata.

Na haɗa shi da tela na, ya aika wa telan N300,000 a asusun telan na banki. Aka ɗinka masa kaya da kuma huluna biyar.

Daga nan ya aiko wani ya karɓar masa a ofishin mu.“Don haka masu ƙoƙarin ɓata mana suna har su na cewa mun karɓi maƙudan kuɗaɗe a hannun Hushpuppi,za su ji kunya.

Domin ba mu tsoma hannun mu cikin dagwalon kuɗaɗen harƙalla ba, kamar yadda wasu ke watsawa.” Inji Kyari.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button