Uncategorized

ABIN TAUSAYI: Ku Kalli Yadda Ƴan Boko Haram Suka ɗauke mata 2 a Monduga — Kwamishinan Ƴan Sanda

ABIN TAUSAYI: Ku Kalli Yadda Ƴan Boko Haram Suka ɗauke mata 2 a Monduga — Kwamishinan Ƴan Sanda

Ƴan Boko Haram sun ɗauke mata 2 a Monduga — Kwamishinan Ƴan Sanda.

Kwamishinan Ƴan Sanda ns jihar Borno, Abdu Umar ya ce ƴan ƙungiyar Boko Haram sun sace wasu mata biyu a ƙauyen Mairari da ke Ƙaramar Hukumar Konduga.

Umar ya bayyana haka ne a wata hira da Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN a Maiduguri, inda ya ce lamarin ya faru ne a ranar 7 ga watan Yuni.

“Da misalin karfe 7:30, wani Ari Mustapha na kauyen Mairari a Konduga, ya bayar da rahoton cewa wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton mayakan Boko Haram ne sun mamaye gidansa tare da yin garkuwa da ‘ya’yansa mata guda biyu.

“Ya ce suna da shekarunsu 26 da 30.

“Ya kuma ce maharan sun sace bijiman sa guda biyu da wasu kayayyaki kafin su gudu,” in ji kwamishinan.

Kwamishinan ƴan sandan ya ce da samun bayanan, an tura tawagar ƴan sanda domin gano inda wadanda a ka sace su ke domin ceto su a kewayen wajen amma abin ya ci tura.

Umar ya ce rundunar za ta kara zage damtse har sai an ceto wadanda lamarin ya rutsa da su tare da sada su da iyalansu.

Kwamishinan ya bukaci jama’a da su riƙa kai rahoto ga jami’an tsaro na kusa da su.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button