News

BIDIYO: Ƴan ISWAP Sun Yi Garkuwa Da Ma’aikacin Lafiya A Jihar Borno

Ƴan ISWAP sun yi garkuwa da ma’aikacin lafiya a Borno

A yau Laraba ne Gwamnatin Jihar Borno ta tabbatar da cewa ƴan ƙungiyar ISWAP sun sace wani maaikacin lafiya da ke aiki a babban asibitin Gubio.

A daren Larabar, da misalin ƙarfe 2:30 na safe ne dai ƴan ISWAP ɗin su kankianhari a Gubio, inda su ka yi awon gaba da kayan abinci da nan fetur a motar kai agaji.

Kwamishiniyar Lafiya ta jihar ce ta tabbatar da afkuwar lamarin ga Kamfanin Daillancin Labarai na Ƙasa, NAN, inda ta ce lamarin abin takaici ne .

A cewar ta, ma’aikacin lafiyar da a ka ɗauke na ɗaya da ga cikin jajurtattun da su ka rage su na aikin duk da haɗarin da ke ciki.

Ta ce Ma’aikatar lafiya za ta sanarwar hukumomin da su ke da ruwa da tsaki a rubuce kamar su rundunar ‘Operation Hadin Kai’.

Kwamishiniyar ta kuma yi fatan Ubangiji ya sa a sake shi salin-alin.

Ga Bidiyon Asha Saurare Lafiya

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button