News

BIDIYO: Ƴan ta’adda sun fara tuntuɓar iyalan fasinjojin jirgin ƙasa da su kai garkuwa da su

BIDIYO: Ƴan ta’adda sun fara tuntuɓar iyalan fasinjojin jirgin ƙasa da su kai garkuwa da su

Ƴan ta’addan da su ka kai hari kan jirgin ƙasa a kan hanyar sa ta zuwa Kaduna da ga Abuja a ranar Litinin, sun fara tuntuɓar iyalan fasinjojin da su ka yi garkuwa da su.

Kamar Yadda Zaku Gani Acikin Bidiyon Dake Kasa, Yan Ta’addan Sun Fara Tuntubar Iyalan Fasinjojin Da Suka Riqe A Hannun Su.

Iyalin wani da ga cikin fasinjojin da ya ke hannun ƴan ta’addan, mai suna Abdullahi, sun ce ƴan fashin dajin sun tuntube su ta wayar salula kuma sun ce musu su shirya biyan kuɗin fansa.

A Cewar Sa Yan Ta’addan Ne Suka Kira Su A Wayar Salula Tare Da Shaida Musu Cewa Sune Suka Sace Dan Uwan Su, Dan Haka Su Shirya Biyan Kudin Fansa.

Jaridar Punch ta rawaito cewa wani Jibreel Khalil, ɗan uwan Abdullahi ɗin ya ce duk da ba su fadi nawa za a basu ba, amma dai ƴan ta’addan sun kira sun kuma ce yana hannun su sannan a shirya biyan kuɗaɗen fansa.

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button