Kannywood News

Bidiyon Yadda Aminu Shariff Momo Ya Sha Ihu A Kasuwa Bayan Ya Amshe Dubu Goma Da Ɗan-garuwa Ya Biya Shi Na Ɓarnar Da Ya Masa

Aminu Shariff Momo Ya Sha Ihu A Kasuwa Bayan Ya Amshe Dubu Goma Da Ɗan-garuwa Ya Biya Shi Na Ɓarnar Da Ya Masa

Jarumi Aminu Sheriff, wanda aka fi sani da Momo ya sha ihu a kasuwar Singa da ke Kano bayan wani ya yi masa barna a motarsa.

Wani bidiyo wanda Tashar Tsakar Gida ta wallafa ya nuna yadda jarumin ke ƙirga kuɗi N10,000 a cikin kasuwa yayin da jama’a su ke yi masa ihu.

Kamar yadda aka gani, ya na sanye ne da babbar riga da hula yayin da wani da ake zargin mai tura kurar ruwa ne ya miƙa masa kuɗin ya amshe, ya kirga, sannan ya zuba a aljihu.

An ga yadda aka fasa masa kwalbar fitilar motarsa inda ake zargin hakan yasa ya tsaya tsayin-daka har sai an biya shi.

Bayan ya amshe kuɗin ya shige mota ne aka dinga yi masa ihu yayin da wasu ke kiransa da “ɗan wahala”.

Lamarin ya fusata matasan waɗanda da alamu su na kallon kamar ya fi ƙarfin amsar kuɗin kuma ko da ma yana da buƙata, bai dace ya amsa a hannun ɗan-ga-ruwa ba.

Ya sha ihu ƙwarai kuma da alamun ko a jikinsa don ba tare da ya nuna ɓacin rai ko kuma ya mayar wa da kowa martani ba yayi shigewarsa mota ya tsere.

– Idon Mikiya

https://youtu.be/s7-h7GgZ-wI

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button