Interviews

Duk Sati Ina Samun Naira Miliyan Ɗaya Da Rabi A Sana’ar Carbin Malam, Inji Ramatu

Duk Sati Ina Samun Naira Miliyan Ɗaya Da Rabi A Sana’ar Carbin Malam, Inji Ramatu

An sami wata mata a ƙauyen Fadima da ke da tazarar kilo mita 6 daga babban birnin Katsina.

Wadda ba a taba samun ƴar kasuwa mai himma kamarta ba a ƙauyen.

Fadima wani garin Hausa-Fulani ne da ke kan titin Katsina zuwa Kano, kafin ka kai garin Eka.

Babbar sana’arsu ita ce noma da kiwon dabbobi Dai Dai Sauran Sana’oin Da baza’a Rasaba.

Ramatu, wata matar aure mai matsakaicin shekaru, wadda kuma ba ta yi karatun boko ba.

Ta fara sana’ar alewar carbin malan bayan aurenta na fari wanda bai jima sosai ba.

Ramatu ta yi jawabi dalla-dalla a game da nasarar da ta samu a cikin sana’arta ta alewar carbin malam.

Ramatu ta ce: “Innata ce ta shigar da ni cikin wannan kasuwancin. Ita ce ta koyar da ni duk abin da na sani da kuma yadda ake hada alewar gargajiyar.”

Za ka yi matukar mamaki a gidan Ramatu idan ka ga yadda ma’aikata sama da 70, ciki har da yara mata da maza, suke aikin haɗa alewar da kunshe ta cikin sauri da ƙwarewa.

Bayan ta gama koya, sai Ramatu ta fara gudanar da sana’ar a karon farko da sikarin naira 400 da kwakwa guda ɗaya.

Bayan ta gama haɗawa sai ta kai carbin malam ɗin wata kasuwa da ke kusa da su domin ta sayar. A haka ta cigaba da sana’ar.

Amma sai kasuwancin ya karye sakamakon rashin ciniki da ƙarancin kuɗi a hannunta.

“Ba wata riba na dinga samu ba a farko. Na sha wahala sosai domin na dinga faɗuwa amma na cigaba da jajircewa.”

Ta ci gaba da cewa, “A lokacin mahaifiyata da kakata suka ƙi taimaka min da bashin wasu kuɗi domin in farfaɗo da sana’ata.

Da na ga ba yadda zanyi sai na sayar da kayan dakina na aure sannan nayi amfani da kuɗin gurin farfaɗo da sana’ata da ta karye.” Inji ta

Bayan shekaru biyar da zuba kuɗin kayan ɗakinta a sana’ar, sai Allah ya sanya albarka a ciki har ta kai ta kere innarta da ta koya mata sana’ar a kafuwa.

Da aka tambaye ta a kan nawa take samu a dukkan rana, sai ta ce, “Ina samun naira dubu dari biyu a kullum.”

Ta kara da fadin cewa, “Ina siyan buhuna 13 na sikari a kullum.

Hakan na nufin kenan Ramatu na siyan sama da buhuna 91 na sikari a duk sati. Bayan nan tana samun ribar naira miliyan 1.4, shi ma a kowanne sati.

A yanzu haka tana sayar da carbin malan ɗinta a dukkan ƙananan hukumomi 34 na jihar Katsina da ma sauran makwabtan jihohi.

A kokarinta na sama wa matasa mata da maza na kauyenta aiki, Ramatu ta ɗauki ma’aikata sama da 80 aiki. Da yawan ma’aikatan nata matasa ne ƴan tsakanin shekara 14 zuwa 25.

A yanzu haka ta faɗaɗa kasuwarta zuwa jihohin Kano, Kaduna da Legas.

Yusuf Iro, mazaunin kauyen Fadima ne, ya bayyana cewa ana kai carbin malam ɗin Ramatu wasu ɓangarorin kudancin Najeriya.

Safiya, wata ma’aikaciyar Ramatu, ta ce, “Tun da na fara aiki da ita, ban kara tambayar iyayena kuɗi ba. Ina amfani da kuɗin da nake samu gurin biyan kuɗin makarantana da na ƴan uwana.”

Ita ma A’isha, ƴar shekara 20, ta bayyana cewa sam yanzu ba ta damun iyayenta a kan su ba ta kuɗi. Tana amfanin da kuɗin da take samu gurin ciyar da iyayenta da kuma biyan kuɗin makaranta.

Kazalika kowanne ma’aikaci yana samun akalla sama da naira 500 zuwa 3000 a rana, amma kuɗin ya dogara da yawan kullin da ka iya haɗawa.

Ramatu ta bayyana cewa ita burinta shi ne ta tallafa wa yara mata da fasahar da za ta taimaka musu gurin samun ɗan kuɗin da za su rufa wa kansu asiri.

Daga karshe ta ce babban kalubalen da take fuskanta shine tsadar kudin sikari, saboda haka take roƙon gwamnati ta sanya tallafi a kai.

Domin ta samu damar ƙara yawan sikarin da take saya. Ta ce hakan zai taimaka mata gurin ƙara samun riba da kuma diban ƙarin ma’aikata.

©Idon Mikiya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button