News

Kullum sai mai ɗaki na ta yi min duka, manomi mai neman saki ya shaida wa kotu

Kullum sai mai ɗaki na ta yi min duka, manomi mai neman saki ya shaida wa kotu

Wani manomi mai suna Williams Famuyibo a yau Laraba ya roƙi wata kotun gargajiya ta Mapo Grade ‘A’ da ke Ibadan da ta raba aurensa da matarsa ​​Sola l, mai shekaru 32 sabo da tana yawan dukansa.

Famuyibo, wanda ke zaune a Ibadan, ya ce ba zai iya jurewa dukan na matar tasa ba.

“tun a watan Janairu na gudu daga gidanmu a watan Janairu.

“Ya mai Shari’a, sabo da rashin mutuncin Sola a gare ni, yanzu ina zaune da yayana ne.

“A gaskiya, ba ni da kwanciyar hankali domin ba ta kula da ni.

“Ina da ƴaƴa biyar kafin na auri Sola a shekarar 1990, amma dukkansu suna zaune tare da sauran ‘yan uwana ne sakamakon halin kyamar Sola,” in ji Famuyibo.

Sai dai kuma Sola ba ta halarci zaman kotun ba kuma babu wani lauya da ya wakilce ta a shari’ar, duk da cewa an kai mata sammaci.

Alƙalin kotun, S.M. Akintayo, ya umurci mai bayar da belin kotun da ya sanar da wanda ake ƙara ranar da za a dage sauraron ƙarar.

Akintayo ta dage sauraron karar har sai ranar 26 ga watan Mayu domin ci gaba da sauraron karar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button