Politics

Rikicin APC a Kano: Uwar jam’iya ta fitar da tsarin raba muƙamai tsakanin ɓangarorin Ganduje da Shekarau

Rikicin APC a Kano: Uwar jam’iya ta fitar da tsarin raba muƙamai tsakanin ɓangarorin Ganduje da Shekarau

Jam’iyar APC ta samar da wani tsari na raba muƙamai tsakanin ɓangarorin Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje da Sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya, Ibrahim Shekarau.

Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa, a ci gaba da zaman sulhu tsakanin ɓangarorin biyu da su ke ta gabza rikicin mallakar jam’iyyar tun bayan kammala zaɓen shugabannin jam’iya, a jiya Asabar ne dai Kwamitin Riƙo na APC ya kira jagororin biyu da su je Abuja domin wata ganawa ta gaggawa.

Bayan tashi da ga taron gaggawar, ƙarƙashin jagorancin Mai Mala Buni, Gwamnan Jihar Yobe, jam’iyyar ta yanke shawarar tura wani kwamiti mai ƙarfi zuwa Kano domin tabbatar da an bi sabon tsarin rabon muƙaman jam’iyyar daidai.

A wata taƙaitacciyar sanarwa bayan taron na jiya Asabar da daddare, mai magana da yawun Shekarau, Sule Ya’u Sule, ya tabbatar da cewa jam’iyyar ta samar da tsarin sanya kowa cikin harkokin jam’iyyar ta APC a Kano.

A cewar Sule, a gobe Litinin za a sanar da duk ɓangarori biyun halin da ake ciki.

“Za a kafa kwamiti mai karfi daga sakatariyar jam’iyyar kuma a tura shi Kano don tabbatar da bin ƙa’ida da aiwatar da tsarin da za a yi a ranar Litinin,” in ji Sule.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button