News

Wata Sabuwa: miƙa Abba Kyari ga NDLEA Na Shirin Sake Ballowa Minista Ruwa

Kamar kowane mako, a yau ma mun yi waiwaiye kan muhimman abubuwan da suka faru a makon da ya gabata tun daga Lahadi 13 ga watan Fabrairun 2022 zuwa Asabar 19 ga wata

Ƴan sanda sun miƙa Abba Kyari ga hukumar yaki da miyagun ƙwayoyi

A makon da ya gabata ne rundunar ƴan sandan Najeriya ta ce ta kama mataimakin kwamishinan ƴan sanda Abba Kyar tare da wasu ƴan sanda huɗu kan zargin ta’ammali da hodar iblis.

Wata sanarwa da rundunar ta fitar da yammacin Litinin ta ce an kama mutanen ne bisa zargin haɗa kai wajen aikata miyagun laifuka, da saɓa ƙa’idar aiki.

Sanarwar na zuwa ne sa’o’i bayan hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya NDLEA ta ce tana neman mataimakin ƴan sandan ruwa a jallo saboda zargin ta’ammmali da hodar iblis.

Kakakin rudunar DSP Olumuyiwa Adejobi ya ce an kama mutanen ne bayan wasu bayanai da hukumar ta NDLEA ta fitar.

A makon da ya gabata ne Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya ASUU ta nemi a soke matsayin farfesa da aka bai wa ministan sadarwa na ƙasar Isa Ali Pantami.

ASUU ta bayyana wannan matsayar ne a ƙarshen taron shugabanninta da aka gudanar ranar Litinin, inda ta ce ɗaga darajar Pantami zuwa matsayin Farfesa haramtacce ne.

Shugaban ƙungiyar Farfesa Emmanuel Osodoke yayin wani taron manema labarai yace “ba yadda za a yi kana minista kuma kana karantarwa a lokaci guda.”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button