News

Yadda Aka kama samari 3 suna dafa kan wata budurwa domin yin tsafin samun kuɗi

Yadda Aka kama samari 3 suna dafa kan wata budurwa domin yin tsafin samun kuɗi

An samu gagarumin tashin hankali a yankin Oke Aregba da ke Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun, bayan da aka kama wasu samari maza su na dafa kan wata budurwa da aka ce budurwar ɗaya da ga cikinsu ce, domin yin tsafin samun kudi.

A cewar rahoton Daily Post, da sanyin safiyar yau Asabar ne, wani mai suna Segun Adewusi, wanda shi jami’in tsaron al’umma ne, ya lura da yadda wasu yara maza huɗu su ke dafa wani abu da ake zargin kan mutum ne a wata tukunyar a gefen hanya.

Rahotanni sun baiyana cewa, nan take mai gadin ya sanar da ‘yan sandan da ke ofishin Adatan, inda suka je wurin da lamarin ya faru domin kama masu dafa kan, inda su ka cafke uku daga cikin yaran, ɗayan kuma ya tsere kafin ƴan sanda su zo wajen.

Wata majiya da ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce yarinyar da aka kashe mai suna Rofiat, mazauniyar Idi-Ape ce; ta kasance budurwa ga wani Soliu, wanda yanzu haka ya na komar ƴan sanda.

An ce Soliu ya yaudari yarinyar ne zuwa ɗakinsa, inda ya riƙe ta ya kuma buƙaci ɗaya da ga cikin abokansa ya yanka ta da wuka.

“Wadanda aka kama sun hada da Wriz Oladeinde mai shekaru 17 daga Kugba, Gafar Luukman mai shekaru 19 daga Kugba da Mustakeem Balogun daga Bode Olude, dukkansu a Abeokuta. Soliu shine saurayin yarinyar, ya gudu, amma daga baya aka kama shi.

“Sun kashe Rofiat, suka yanke mata kai, suka tattara gawar mara kai a cikin buhu sannan suka fara kona kan a tukunya. Sun gaya wa ’yan sanda a gaban taron jama’a cewa suna so su yi amfani da shi wajen yin tsafin samun kuɗi.

“’Yan sanda sun tafi da gawar zuwa dakin ajiyar gawa,” wata majiya ta shaida wa wakilinmu ranar Asabar.

A cikin wani ikirari na faifan bidiyo, Mustakeem Balogun, ya ce, “Mun so mu yi amfani da kanta ne kawai don yin ibadar kudi. Soliu ya shake ta, ya ce in taimake shi, muka yanke mata kai.”

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button