News

BIDIYO: Dakarun Nijeriya sun kama manya-manyan sansanonin ƴan ta’adda a Sambisa tare da ƙwace makamai

Dakarun Nijeriya sun kama manya-manyan sansanonin ƴan ta’adda a Sambisa tare da ƙwace makamai

Sojojin Rundunar ‘Operation Hadin Kai’, OPHK, sun samu gagarumar nasarar kame wasu manya-manyan sansanonin ƴan ƙungiyar ISWAP a Ukuba/Camp Zairo a dajin Sambisa.

Daraktan yaɗa labarai na rundunar sojin Nijeriya, Bernard Onyeuko, a wata sanrwa da ya fitar a yau Juma’a a Abuja, ya ce dakarun sun kuma ƙwace makamai da ga gurin ƴan ta’addan.

Onyeuko ya ce rundunar ta samu wannan nasara ne a jiya Alhamis a wani sintiri da su ka yi mai sunan “sintirin share sahara”.

Ya ce dakarun ne su ka gano ƴan ta’addan sannan su ka kwace sansanonin na su, inda bayan sun tsere, sai dakarun su ka kwashe makaman su.

Ya ƙara da cewa bayan bincike mai zurfi da kuma kewaye wajen, sai jajirtattun sojojin mu su ka su ka dirar musu inda su ka tsere, su kuma dakarun su ka kwashe makaman su.

Daga makaman sun haɗa da Tankar yaƙi, bindiga mai tsayin 155m, bindigar Bofors, Tirela guda ɗaya, bindiga mai tsayin 122mm da bindigogi masu tsayin 105mm.

Ga Bayanin Nan Dakuma Yadda Lamarin Ya Afku

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button