News

BIDIYO: Limamin Masallacin Juma’a ya ajiye limanci sabo da zai tsaya takara a Katsina

Limamin Masallacin Juma’a ya ajiye limanci sabo da zai tsaya takara a Katsina

Imam Muhammad Hashim, Limamin Babban Masallacin Juma’a na GRA a Jihar Katsina ya ajiye muƙamin limancin sabo da zai tsaya takara.

A wasiƙar ajiye limancin da ya rubuta, mai ɗauke da kwanan watan 24 ga Maris, Mallam Hashim ya yi addu’ar Allah Ya rubuta masa ayyukan alherin da ya yi a cikin ayyukansa.

Wani ɓangare na wasiƙar, wacce Daily Nigerian Hausa ta gani ya ce, ” i Muhammad Hashim (Liman) na ake muƙami na na limancin Babban Masallacin Juma’a na GRA sabo da tsaya wa takara da zan yi.

“Ina fatan Allah SWT Ya rubuta mana ayyukan mu na alheri a cikin ibadun mu da mu ka gabatar, Ya yafe mana kusa-kuren mu Amin.

A cikin wasiƙar, mai ɗauke da sa hannunsa, Hashim ya nemi yafiyar ƴan kwamitin masallacin da ma al’umma baki ɗaya.

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button