News

‘Ƴan bindiga sun kona wata motar fasinja dauke da mutum 42 a Sokoto’

‘Ƴan bindiga sun kona wata motar fasinja dauke da mutum 42 a Sokoto’

Rahotanni daga jihar Sokoto da ke arewacin Najeriya na cewa ‘yan bindiga sun kona wata motar fasinja dauke da mutum 42.

Rahotannin sun ce fasinjojin sun fito ne daga karamar hukumar Sabon Birni da ke jihar domin yin ƙaura zuwa wasu yankunan Najeriya, saboda ta’azzarar ayyukan ‘yan bindiga a inda suke.

Wasu shaidu sun cewa BBC lamarin ya faru ne da misalin karfe 9 na safiyar ranar Litinin.

“Motar ɗauke da fasinjojin ta tashi daga Sabon Birni, ta yi tafiyar da bai fi kilomita shida ba zuwa kauyen Gidan Bawa inda wannan masifa ta afka mata,” kamar yadda wadanda suka yi aikin ceton suka bayyana wa BBC.

BBC ta yi ƙoƙarin jin ta bakin rundunar ƴan sandan jihar, amma haƙarmu ba ta ci cimma ruwa ba, ko da muka kira kakakin, wayarsa a kashe take.

Kazalika mun kira kwamishinan tsaro na jihar har sau uku shi ma bai ɗauka ba.

Yankin arewa maso yammacin Najeriya na ɗaya daga cikin yankunan da suka fi fama da matsalar tsaro a Najeriya, sai dai a lokuta da dama gwamnatocin yankin na cewa suna iya kokarinsu domin tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin al’umarsu, abin da al’umar ke cewa ba sa gani a kasa.

Za mu ci gaba da kawo muku ƙarin bayani kan labarin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button