News

Pantami Ya Ba Ni Mamaki Matuqa Na Bujirewar Shi Kan Karin Kashi 5 Cikin 100 Na Kiran Waya, Cewar Ministar Kudi

Pantami Ya Ba Ni Mamaki Matuqa Na Bujirewar Shi Kan Karin Kashi 5 Cikin 100 Na Kiran Waya, Cewar Ministar Kudi

DAGA Abubakar A Adam Babankyauta

Ministan kudin Nijeriya Zainab Ahmad Shamsuna ta ce za su kara harajin kashi 5 cikin 100 na kiran waya a Nijeriya duk da Ministan sadarwa Sheikh Pantami ya kalubalanci karin harajin.

Kamar yadda muka samu labari daga majiyar mu cewa ministan kudi da kasafin kudi da tsarin Zainab Ahmed shamsuna ta ce babu gudu babu ja da baya kan batun karin kashi 5 cikin 100 na harajin waya.

Zainab ta ce majalisar tarayyar Nijeriya da majalisar zartarwa na tarayya, FEC, duk sun amince da karin kafin Shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan sabuwar dokar.

Ministan ta kuma soki maganar da ministan sadarwa da tattalin arziki, Farfesa Isa Ali Pantami ya yi kan harajin tana mai cewa ya san da maganan harajin da kuma dalilin hakan.

Ministan ta kuma soki rashin amincewa da Ministan Sadarwa da tattalin Arzikin zamani, Farfesa Isa Ali Pantami ya yi da harajin tana mai cewa a matsayinsa na mamba na Majalisar zartarwa, yana da masaniya kan karin harajin da dalilin yin hakan tun kafin a aiwatar.

A makon da ya gabata ne Isa Pantami, ministan sadarwar da tattalin arzikin zamani ya soki shirin na aiwatar da karin harajin kashi biyar kan harkokin sadarwa a Nijeriya.

Zainab Ahmed, ministan kudi, kasafin kudi da tsarin kasa, ta ce gwamnatin tarayya tana cigaba da shirin aiwatar da karin kashi biyar na haraji kan ayyukan sadarwa kuma babu abun da zai hana karin wannan harajin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button