News

BIDIYO: An ɗage shari’ar Ɗansarauniya saboda ta haɗe da shari’ar Sheikh Abduljabbar Kabara.

An ɗage shari’ar Ɗansarauniya saboda ta haɗe da shari’ar Sheikh Abduljabbar Kabara.

Basira Haruna Sadiq

An ɗage zaman shari’ar da Kotun majistiri mai lamba 58 ta sanya za ayi gobe dan cigaba da saurararen Shari’ar tsohon kwamishinan ayyuka na Kano Engr Muaz Magaji saboda ta haɗe da ranar da za ayi shari’ar Malamin Addinin Musulunci Sheikh Abduljabbar Kabara a babbar kotun shari’ar Muslunci dake zaman ta a kofar kudu, a Kano.

Hakan na kunshe cikin wata Sanarwa da Barista Wada A Wada ya sanya wa hannu, wanda shine Lawya mai gabatar da kara a Shari’ar, yana bayyana cewa Mai Shari’a Aminu Gabari ne ya ɗage zaman daga 3 ga wata zuwa 4 ga watan na Fabrairu sakamakon jami’an tsaron da zasu kasance a wajen shari’ar Malam Abdujabbar sune zasu kawo Muaz Magaji Kotu Lokacin da za ayi shari’ar sa.

A watan da ya bata mai Shari’a Ibrahim Sarki Yola ya sanya ranar 3 ga watan Febrairu dan ci gaba da Shari’ar Abduljabbar Nasiru Kabara, wanda yayi daidai da ranar da Mai Shari’a Aminu Gabari ya sanya dan cigaba da Shari’a Muaz Magaji.

Hakan yasa Kotun ta yi la’akari da cewar ana jibge jami’an tsaro da dama a yayin Shari’ar Sheikh Abduljabbar Kabara, haka zalika ita ma Shari’ar Ɗan sarauniyar na da buƙatur a jibge mata jami’an tsaro.

Saboda haka na dage shari’ar ɗan sarauniya sai ranar juma’a 4/2/2022 da Muslim karfe 2:30 na rana a kotu mai lamba 58 dan cigaba da saurararen Shari’ar.

An gurfanar da Ɗan sarauniyar ne bisa zargin aikata laifin cin mutuncin gwamnan Kano Dr Abdullahi Ganduje, da kuma kalaman da aka iya haifar da tunzuri, da yada karya a shafinsa na Facebook.

Jarida Radio
2/2/22

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button