News

BIDIYO: Shekara ɗaya bayan mutuwar shugaban ƙungiyar Boko Haram Abubakar Shekau ana ta samun ƙaruwar ƴaƴan ƙungiyar da ke mika wuya ga sojojin Najeriyar.

Shekara ɗaya bayan mutuwar shugaban ƙungiyar Boko Haram Abubakar Shekau ana ta samun ƙaruwar ƴaƴan ƙungiyar da ke mika wuya ga sojojin Najeriyar.

Tun bayan mutuwar jagoran ƙungiyar ake ganin lagon ƙungoyar ya karye, kuma ruɗani ya kutsa cikinta, har wasu daga cikin ƴaƴanta da jigoginta suka shiga miƙa wuya ga sojojin Najeriya.

A ranar 19 ga watan Mayun 2021 ne aka fara samun labarin mutuwar Abubakar Shekau, mutumin da ya shafe shekara 12 yana jan ragamar kungiyar masu tayar da ƙayar baya ta Boko Haram, wacce ta dinga kai munanan hare-hare a Najeriya da Nijar da Kamaru har ma da Chadi.

Kafin lokacin mutuwar Shekau a watan Mayun 2021, a kalla sau hudu ana ba da rahoton mutuwarsa, amma yana fitowa yana ƙaryata hakan.

Tun da ya karɓi ragamar shugabantar ƙungiyar Boko Haram a shekarar 2009, ana yi wa Shekau kallon mara tausayi saboda yadda ya addabi al’ummar arewa maso gabashi, kai har ma da arewa maso yammaci da kuma arewa ta tsakiyar Najeriya, da ma wasu sassan, wadanda suka sa ya yi ƙaurin suna.

A yayin da yake cika shekara daya da barin duniya, BBC Hausa ta yi waiwaye kan wasu munanan hare-hare 12 da Shekau ya jagoranta cikin 12 da ya yi yana jan ragamar ƙungiyar, waɗanda suka daga hankula a duniya.

https://youtu.be/8PvodI-dHqM

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button