Politics

Rikicin APC a Kano: Ganduje da Barau sun bazama gidan Garo domin hana shi ficewa daga APC

Rikicin APC a Kano: Ganduje da Barau sun bazama gidan Garo domin hana shi ficewa daga APC

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje da Sanata mai wakiltar Kano ta Arewa Barau Jibrin sun kai ziyarar bazata ga mataimakin dan takarar gwamna na jam’iyyar APC, Murtala Garo da tsakar daren Alhamis.

DAILY NIGERIAN ta tattaro cewa gwamnan, ya yi fitar sirri ce ba tare da ayarin motoci ba, inda ya ziyarci gidan Garo ɗin da ke ayarin gidajen Railway domin lallashin sa ya ci gaba da zama a jam’iyyar APC.

Wata majiya da ke da masaniya kan ziyarar ta ce Ganduje ne ya fara zuwa gidan kafin Barau Jibrin ya same shi a can.

Majiyar ta kara da cewa su ukun sun yi ganawar sirri.

A kwanakin baya ne Garo ya nuna damuwarsa kan janyewar Gwamna Ganduje daga takarar Sanata ya bar wa Sanata Jibrin, wanda babban ɗan adawarsa ne a siyasa.

A wani mataki na nuna rashin amincewa da matakin, da kuma gazawar gwamnan wajen hana ficewar da a ke ta yi da ga jam’iyyar, Garo ya ƙaurace wa harkokin gwamnatin.

Majiyoyi sun ce tsohon kwamishinan kananan hukumomin mai karfin iko na iya sauya sheka zuwa PDP domin yiwa surukin sa, Atiku Abubakar aiki a takararsa ta shugaban kasa.

Jam’iyyar a jihar na cikin mawuyacin hali, inda jiga-jigants ke ta ficewa kuma haka na iya kawo mata nakasu a nasarar zaben.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button