Politics

SHARI’AR GWAMNAN KANO: Ayodele Yace Gawuna Ne Zai sake Yin Nasara Akan Abba Kabir Yusif A Kotun Allah Ya Isa.

SHARI’AR GWAMNAN KANO: Ayodele Yace Gawuna Ne Zai sake Yin Nasara Akan Abba Kabir Yusif A Kotun Allah Ya Isa.

Primate Babatunde Elijah Ayodele, ya yi hasashen yadda za a kwashe a kotun koli tsakanin APC da NNPP a jihar Kano.

Ayodele ya ce Nasiru Gawuna ne zai sake yin nasara a kan Abba Gida Gida Ko An Sake Komawa kotun Allah ya isa.

Kotun zaben gwamnan jihar Kano dai ta tsige Gwamna Abba Kabir Yusuf inda ya daukaka kara zuwa kotun gaba.

Ayodele ya bayyana hakan ne a cikin wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Laraba, 18 ga watan Oktoba.

“Kuma na Tabbata koma menene, APC ce za ta yi nasara a kotun koli, sai dai idan alkalan sun yi murdiya. Wannan shine kawai abun da ke ciki.” A Cewar Ayodele

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button