Politics

SHARI’AR ZABEN KANO: A Yau Kotun ɗaukaka ƙara za ta fara sauraron ƙarar zaɓen gwamnan jihar kano

A Yau Kotun ɗaukaka ƙara za ta fara sauraron ƙarar zaɓen gwamnan jihar kano

Kotun ɗaukaka ƙara za ta fara sauraron ƙarar zaɓen gwamnan jihar kano

Kotun ɗaukaka ƙara da ke zaman ta a Abuja za ta fara sauraron ƙarar da gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf da jam’iyyarsa ta NNPP suka shigar gabanta, don ƙalubalantar hukuncin kotun sauraron ƙorafin zaɓe ta jihar.

Daukaka ƙarar dai ya biyo bayan hukucin da kotun sauraran ƙararaki zaɓen gwamann jihar ta yi a ranar 23 ga watan Satumbar da ya gabata, inda ta bayyana Dr Nasir Yusuf Gawuna a matsayin wanda ya yi nasara a zaben gwamnan da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris na 2023.

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf da jam’iyyar sa ta NNPP ne dai suka ɗaukaka ƙara bayan da kotun saurarar ƙararrakin zaben gwamnan jihar ta soke ƙuri’u 165,663 daga jimillar waɗanda suka samu a zaɓen da ya gabata.

Kotun ta ce ta soke kuri’un ne sakamakon rashin sanya hannu da stamfi a kan ƙuri’un da hukumar zaɓen ƙasar ta INEC ba ta yi ba.

A wata sanarwa da kotun ɗaukaka ƙarar ta fitar ta ce za a fara sauraron ƙarar ne a kotun da ke birnin tarayayr Najeriya Abuja a ranar litinin.

Cikin wanɗa Abba Kabir Yusuf ɗin ke ƙara sun haɗa da dan takarar gwamna na APC a Kano a zaben da ya gabata Dr. Nasir Yusuf Gawuna da jam’iyyar APC ɗin da hukumar zaɓen ƙasar ta INEC.

Gwamna Abba Kabir Yusuf na neman kotun ɗaukaka ƙarar ne da ta yi watsi da hukuncin kotun ƙararrakin zaɓen gwamna ta jihar Kano, wadda ta soke masa ƙuri’u tare da bayyana Dr Nasir Yusuf Gawuna a matsayin wanda ya yi nasara a zaben gwammnan jihar a hukuncin da ta zartar ta kafar zoom a ranar 20 ga watan satumban 2023.

Abba Kabir ya ce hukuncin ƙaramar kotun na cike da kura-kurai inda a yanzu za a zura ido a ga hujjojin 43 da ya ce ya gabatar wa kotun daukaka karar.

Tun dai bayan yanke hukuncin kotun sauraren ƙararrakin zaben, jam’iyyar APC a Kano da ɗan takararta Nasir yusuf Gawuna suka ce ba su da wata fargaba, na zuwa babbar kotun.

Bayan hukuncin kotun sauraron ƙararakin zaɓe an yi ta musayar yawu tare da tayar da jijiyoyar wuya kan shari’ar.

Hukumar Zaɓen Najeirya ta INEC ta dai bayyana Abba Kabir Yusuf a mastayiun wanda ya yi nasara a zaɓen da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris ɗin sharar nan, da kuri’u miliyan 1,019,602, ya yin da Naisr Yusuf Gawuna ya sami ƙauri’a 890,705.

Sai dai bayan da kutun saurar ƙarar zaɓen gwamna ta soke ƙuri’u 165,663, ƙuri’un Abba Kabiru sun koma 853, 939, wanda hakan ya yi ƙasa da ƙuri’un da Naisr Yusuf Gawuna ya samu da 30,000.

Kano ta kasance jiha ta biyu mafi yawan masu kada kuri’a a Najeriya.

Shari’ar ta gwamnan jihar kuma na jan hankali yan Najeriya musamman saboda girman hamayya da ke tsakanin jam’iyyun APC da NNPP da irin rawar da iyayen gidajensu ke takawa a siyasar Najeriya.

Dukkanin bangarorin biyu na ikirarin samun nasara a shari’ar, amma abin jira a gani dai shi ne yadda shari’ar zata kaya, kuma lokaci ne kadai zai tabbatar da wanda hukuncin za iyi wa dadi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button