Politics

Tirqashi: Sabuwar Gwamnatin Tunibu Za Ta Yi Gadon Tulin Bashi

Rahoton da Ofishin kula da basussuka ya fitar na kwata na hudu na shekarar 2022 ya nuna cewa jimlar bashin da ake bin Najeriya a wannan lokacin ya haura Naira Triliyan 46.25

Yayinda ake kirga ‘yan kwanaki kalilan Gwamnatin Shugaba Mohammadu Buhari ta nade nata inata ta bar gadon mulki, an gano cewa Gwamnati mai jiran gado za ta gaji yawan basussukan da ake bin Najeriya da ya haura sama da Naira triliyan 80. Wannan jimlar ta hada da wasu kudade da Majalisar Dattawa ta amince da kashe su da aka yi cikin shekaru 10 da suka wuce da aka yi wa lakabi da “Ways & Means” a turanci,
Masana tattalin arziki da ma wasu ‘yan kasa sun nuna damuwa kan haka.

Daga ciki, jimlar bashin cikin gida ya kai Naira triliyan 27.55 yayin da bashi na waje ya kai Naira triliyan 18.70 wato kwatankwacin dalar Amurka biliyan 41.69 (USD 41.69BN) ya zuwa watan Disamba na bara.

Masanin tattalin arziki Yusha’u Aliyu wanda ya yi nazari akan al’amarin ya ce wadannan basussuka da kasar ta ciwo a cikin shekaru 10, sun fi ta’azara ne acikin shekaru takwas da suka gabata sakamakon cewa kasafin kudinda ake yi a kasar yana da fadi , wanda a 2022 da kuma 2023 kasafin kudin da akayi ya kai kusan triliyan 20, wanda gibinsa yana dayawa kuma sai an nemo kudade da dama sannan a aiwatar da shi. Haka kuma akwai dalilai da ya sa jihohi da dama a cikin kasa, an bude masu kokofi da suka samo kudade daga kasashen waje domin aiwatar da wasu aiyuka, wanda ya kai ga kusan kashi 95 ko 96.3 na kudadenda aka samo wanda ake amfani da su wajen biyan basussuka a cewar babban bankin duniya.

Sai dai kuma, masanin tattalin arzikin kasa da kasa Shuaibu Idris Mikati yana mai ra’ayin cewa bazi yiwu a ce ba za a ci bashi ba gaba daya, domin bashi hanji ne kuma yana cikin kowa, har kasashen da suka cigaba kamar su Amurka, Birtaniya, Jamus da Kasar Afirka ta Kudu, da ita kanta kasar China mai bada basusuka. Mikati ya ce cin bashi ba abind Allah wadarai ba ne domin akwai wasu kasashen idan sun je neman bashin ma ba a ba su, saboda da haka duk da tulin bashin da Najeriya ta ciwo a ce ana bata, abin godiya ne.

Mikati ya kuma shaidwa wakiliyar Muryar Amurka Medina Dauda cewa, abin lura shi ne, jami’an Gwamnatin tarayyar Najeriya suna bayanin cewa ba bashi ne matasalar Najeriya ba, saboda bashin da kasar ta karbo duk bai wuce kaso 27 zuwa 30 cikin dari ba idan aka dangana shi da karfin tattalin arzikin Najeriya.

mu bai wuce kashi 27 zuwa 30 da wani abu cikin 100 ba na karfin arzikin mu (wato GDP a turanci) da akan duba a kowace shekara. Mikati ya ce masana tattalin arziki sukan kara duba alkaluman kididdiga, kaman wato a farko in mutum ya dubi bashin da Najeriya ta ci, sai a ce eh, akwai hanyoyi da kuma dama da Najeriya za ta kara cin bashin,amma duk wanda ya ci bashi zai so ya biya da kansa,abin tambaya ita ce, ta ina mutum zai biya bashin da ya ci?

Sai dai kuma, Dokta Sa’ad Usman shi ma masanin tattalin arziki ya ce dole ne Mahukunta a Najeriya su dinga sara suna duban bakin gatari musamman a kan batun ciwo bashi.

Sa’ad ya ce korafe korafe da ake yi akan basussuka da Najeriya ta ci,daidai ne domin idan basussukan sun yi wa kasa yawa, zai zame mata illa saboda dole ne a biya uwar kudi da kuma kudin ruwa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button