News

Bidiyon Yadda Ƴan Najeriya suke cashewa sabbin kudin naira

Bidiyon Yadda Ƴan Najeriya suke cashewa sabbin kudin naira

Tun bayan da Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya ƙaddamar da sabbin takardun naira da aka sauyawa fasali, ƴan ƙasar suka yi wa batun ca ta hanyar bayyana ra’ayoyinsu kan hakan.

Shafukan sada zumunta na Facebook da Tuwita da Instagram da Tiktok da ma Whatsapp sun zama wuraren da ba a zancen komai sai na sabbin kudin.

Da yawan mutane sun nuna rashin jin dadinsu kan tsarin sabbin kuɗin, suna cewa ba su zaci haka sauyin zai zo ba.

An ƙaddamar da kuɗaɗen ne a wajen taron mako-mako da ake yi a fadar shugaban ƙasar a Abuja a ranar Laraba.

Shugaba Buhari ya ce sababbin takardun kuɗin za su taimaka wa Najeriya ta wajen warware matsaloli da dama da suke addabar ƙasar.

A shafukan Facebook da Tuwita, sai da ya zama shi ne babban batun da aka fi tattaunawa a kansa tun daga ranar Laraba har zuwa wayewar garin Alhamis.

Tiktok ma ba a bar shi a baya ba, don yawanci matasa ƴan Najeriya da ke amfani da shafin sun mayar da hankali ne yin raha da barkwanci kan lamarin.

https://youtu.be/17ZZ27kFx-E

Yayin da Whatsapp da Instagram suka zama wajen da kusan kowa ya dinga wallafa sabbin kudin a sitatus (status) da sitori (story) ɗinsu.

Me aka dinga cewa?
A shafin Tuwita a ranar Laraba an yi amfani da maudu’in #Naira sau fiye da 200,000, yayin da a ranar Alhamis ma aka ci gaba da amfani da shi har sau fiye da 136,000.

Facebook kuwa a ranar Larabar sama da mutum 300,000 ne suka yi ta tattauna zance har zuwa Alhamis.

Ko a shafinmu na BBC Hausa Facebook, wanda yana ɗaya daga cikin shafukan da suka fara saka hotunan sabbin kudin, inda alƙaluma suka nuna cewa mutum miliyan 1,300,040 suka gani, yayin d ayawan waɗanda suka so suka yaɗa suka kuma yi tsokaci ya kai mutum 309,000, kamar yadda za a iya gani a ƙasa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button