Religion

BIDIYO: Hon. Kawu Sumaila Ya Baiwa Budurwa Yar Shekara 18 Wadda Ta Rubuta Alkur’ani Daka, Adai-daita Sahu

BIDIYO: Hon. Kawu Sumaila Ya Baiwa Budurwa Yar Shekara 18 Wadda Ta Rubuta Alkur’ani Daka, Adai-daita Sahu

Hon. KAWU SUMAILA OFR. YA BAWA GWANA YASIRA SALISU KYAUTAR SABON ADAIDAITA SAHU.🛺🛺🛺

Hon. Abdurrahman Kawu Sumaila Ofr, ya bawa Gwana Yasira Salisu Mahaddaciyar Al-Qur’ani Wacce ta Rubuta Al-Qur’ani Mai Girma da hannun ta ya bata kyautar Sabon Adaidaita Sahu.

Hon Yace Yabata Wannan Babur Ne domin ƙarfafa mata Guiwa tare da ƙarawa yara da matasa kishin koyon karatun Al-Qur’ani da Haddarsa.

Iyayen Gwana Yusra da malamanta suna miqa godiya ta musamman ga mallam kawu sumaila.

A madadin yan uwa Ahlul Qur’an muna taya Gwana Yusra murna sosai Allah Ya Sanya mata Albarka a karatun ta yasa ya zamo hanyar tsira duniya da lahira.

shi kuma hon. kawu sumaila Allah ya saka masa da alheri da irin wannan hidima da yakewa Al-Qur’ani da masu Al-Qur’ani.

Allah yasa sauran yan siyasarmu suyi koyi da shi, Allah Ya Saka Masa da alheri Allah ya biya masa bukatun sa na Alheri.

Allah ya kara masa daraja da daukaka a duk lamuran sa Amin. 🤲🏽🙏🏼

📸Gwani Anwar.

✍🏼Daga Shafin Mu Koma Tsangaya

https://youtu.be/CMkJhw6SgNs

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button