Religion

BIDIYO: Datti Assalafy Yayi Karin Haske Kan Allah Ya Isar Da Sheikh Idris Yayiwa Su Bala Lau Da Kabiru Gombe Na Saka Baki A Belin Sa

BIDIYO: Datti Assalafy Yayi Karin Haske Kan Allah Ya Isar Da Sheikh Idris Yayiwa Su Bala Lau Da Kabiru Gombe Na Saka Baki A Belin Sa

A cikin jawabin, zaku ji inda Malam Idris ya kama sunana Datti Assalafiy da sunan Sheikh Dr Ibrahim Disina yace mu biyu ne ya bawa sako na amana.

Akan mu isar zuwa ga Shugabannin Izala cewa bai yadda su saka baki a sake shi ba.

Idan suka saki baki Allah Ya isa bai yafe musu ba, Malam ya kirani ne a wayar Dalibinsa da ya kai masa ziyara a kurkuku.

Lokacin da na fara wallafa wani rubutu akan albishir su Sheikh Bala Lau zasu zo Bauchi akan case din Malam.

Duk da ban fitar da abin ba amma an gane sakon ya isa inda banyi tsammani ba, daga bisani nayi hiding posting din

To bayan munyi magana da Malam a kurkuku ya bani sako na amana, sai nan take na dau waya na kira wanda zai isar da sako gurin su Shugaba Sheikh Bala Lau.

Na fada masa sakon Malam, sai yace to Malam Datti menene shawararka? sai nace masa to ga shawara kamar haka:

👇
Ka fada wa su Shugaba Malam Bala Lau cewa tunda sun yi niyyar zuwa to kar su fasa, suyi don Allah ba don Malam ba.

Kuma suyi don kare akida ta sunnah, sannan suyi hakuri da duk abinda zasu ji daga bakin Malam Idris idan ya fito.

Akwai sirrin da Malam Idris ya fada min tun yana kurkuku, shi Malam Idris da kuka ganshi baya magana sai ya taki hujja, shiyasa ya gagari makiyansa.

Tabbas an cutar da Malam Idris an masa bita da kulli, kuma yayi hakuri matukar hakuri sannan yayi karamci

Duka Malamannan nan suna da dumbin alheri a tare da su, amma suna da inda suka gaza a matsayinsu na ‘yan Adam.

Da Malam Idris da su Shugaba Sheikh Abdullahi Bala Lau duka namu ne, a kan kare da’awarsu na Sunnah sai inda karfin mu ya kare.

Ni dai shawaran da nake bawa ‘yan uwana Ahlussunnah dake cikin kungiyar Izala da wadanda suke tare da Malam Idris ‘yan media da suke ta rubuce-rubuce shine kuyi hakuri ku dena martani akan wannan abin, shirun ku shine alheri ga Malamanku.

Kuma idan kunga Malamai suna fada to bai kamata ku sa baki ba, Malaman sun fimu sanin kansu.

Zaku ga na wallafa wani rubutu, nace yana daga manufar kafa kungiyar Izala shine shiga lamarin duk wanda yake da’awar Sunnah ko da yana fada da Kungiyancin kungiyar.

Shi Malam Idris ba fada yake da Malaman Izala ba, yana fadane da Kungiyancin kungiyar, kuma babu wani Ahlussunnah da ya isa ya nesanta kansa da Izala a gurin mushrikai da ‘yan bidi’ah.

Sannan da yau wani dan bidi’ah zai fito yace zai cutar da Sheikh Abdullahi Bala Lau ko wani Malamin Sunnah da yake da sabani da Malam Idris, ina mai rantsuwa da Girman Allah sai inda karfin Malam Idris ya tsaya

Kowa yayi hakuri ya kawar da kai, hadin kai muke fata tsakanin ‘yan uwa Ahlussunnah

Allah Ya mana muwafaka duniya da lahira Ya shiryar da matsafa da ‘yan bidi’ah

KU DENA SHIGA FADAN MALAMAI

Yau kwana biyu kenan bayan Dodon matsafa da ‘Yan bidi’ah na Afirka Sheikh Dr Idris Abdul-Aziz Bauchi ya fito daga gidan yari, Malam yayi wasu maganganu wanda ya shafi Kungiyar Izala, ake ta muhawara a dandalin Facebook, ‘yan Izala suna cewa Malam bai kyauta ba

Zan saka audio na cikakken jawabin da Malam Idris Abdul-Aziz Bauchi yayi da daddare bayan ya fito daga kurkuku a Telegram group a wannan Link https://t.me/+SdOQ7Dw3-zmK-2-C

Da WhatsApp guda biyar suma da link dinsu kamar haka:
(1) https://chat.whatsapp.com/Bf916Kb50NPFDViy95aouB

(2)
https://chat.whatsapp.com/BJVg61opcmoAGZTFB9jBfp

(3) https://chat.whatsapp.com/EJ7jyAzjnkqE3rtz3h7Ak7

(4) https://chat.whatsapp.com/GfUEFYJ88iTHkh2qob2usm

(5) https://chat.whatsapp.com/FehGN6qQRO93nGaD091zxF

A cikin jawabin, zaku ji inda Malam Idris ya kama sunana Datti Assalafiy da sunan Sheikh Dr Ibrahim Disina yace mu biyu ne ya bawa sako na amana akan mu isar zuwa ga Shugabannin Izala cewa bai yadda su saka baki a sake shi ba, idan suka saki baki Allah Ya isa bai yafe musu ba, Malam ya kirani ne a wayar Dalibinsa da ya kai masa ziyara a kurkuku lokacin da na fara wallafa wani rubutu akan albishir su Sheikh Bala Lau zasu zo Bauchi akan case din Malam, duk da ban fitar da abin ba amma an gane sakon ya isa inda banyi tsammani ba, daga bisani nayi hiding posting din

To bayan munyi magana da Malam a kurkuku ya bani sako na amana, sai nan take na dau waya na kira wanda zai isar da sako gurin su Shugaba Sheikh Bala Lau, na fada masa sakon Malam, sai yace to Malam Datti menene shawararka? sai nace masa to ga shawara kamar haka:
👇
Ka fada wa su Shugaba Malam Bala Lau cewa tunda sun yi niyyar zuwa to kar su fasa, suyi don Allah ba don Malam ba, kuma suyi don kare akida ta sunnah, sannan suyi hakuri da duk abinda zasu ji daga bakin Malam Idris idan ya fito

Akwai sirrin da Malam Idris ya fada min tun yana kurkuku, shi Malam Idris da kuka ganshi baya magana sai ya taki hujja, shiyasa ya gagari makiyansa, tabbas an cutar da Malam Idris an masa bita da kulli, kuma yayi hakuri matukar hakuri sannan yayi karamci

Duka Malamannan nan suna da dumbin alheri a tare da su, amma suna da inda suka gaza a matsayinsu na ‘yan Adam, da Malam Idris da su Shugaba Sheikh Abdullahi Bala Lau duka namu ne, a kan kare da’awarsu na Sunnah sai inda karfin mu ya kare

Ni dai shawaran da nake bawa ‘yan uwana Ahlussunnah dake cikin kungiyar Izala da wadanda suke tare da Malam Idris ‘yan media da suke ta rubuce-rubuce shine kuyi hakuri ku dena martani akan wannan abin, shirun ku shine alheri ga Malamanku, kuma idan kunga Malamai suna fada to bai kamata ku sa baki ba, Malaman sun fimu sanin kansu

Zaku ga na wallafa wani rubutu, nace yana daga manufar kafa kungiyar Izala shine shiga lamarin duk wanda yake da’awar Sunnah ko da yana fada da Kungiyancin kungiyar, shi Malam Idris ba fada yake da Malaman Izala ba, yana fadane da Kungiyancin kungiyar, kuma babu wani Ahlussunnah da ya isa ya nesanta kansa da Izala a gurin mushrikai da ‘yan bidi’ah

Sannan da yau wani dan bidi’ah zai fito yace zai cutar da Sheikh Abdullahi Bala Lau ko wani Malamin Sunnah da yake da sabani da Malam Idris, ina mai rantsuwa da Girman Allah sai inda karfin Malam Idris ya tsaya

Kowa yayi hakuri ya kawar da kai, hadin kai muke fata tsakanin ‘yan uwa Ahlussunnah

Allah Ya mana muwafaka duniya da lahira Ya shiryar da matsafa da ‘yan bidi’ah

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button