ABIN A YABA: Yana sana’ar P.O.S za’a tura masa 10,000 aka tura masa miliyan 10 yaje wajen yan sanda cikiyar mai kuɗin.
Wannan bawan Allah da kuke gani sunan sa, Muhammadu Sani Abdurrahaman dake sana’ar P.O.S a Round about na Baban Gwari a jihar Kano.
Matashin mai shekaru 36 a shekarar da ta gabata ne wani babban mutum yaje wajen sa don cirar 10k sai yai mantuwa ya tura miliyan 10, tun lokacin wannan bawan Allah yaje ya kaiwa yan sanda rahoton kuɗin da aka tura masa kasancewar mai kuɗin bai neme shi ba, shi kuma bai san wanda ya tura kuɗin ba.
Alamu sun nuna mai kuɗin yafi ƙarfin su shine dalilin da yasa har bai nemi kuɗin nasa ba, domin da aka tambayi mai kuɗin yace abubuwa ne sukai masa yawa shi kuma ya manta a inda ya tura kuɗin kawai ya cigaba da harkokin sa.
Sai dai sakamakon bada cikiya da wannan bawan Allah yai a hukumar yan sandan jihar Kano sai aka ce masa yaje za’a neme shi idan an ga mai kuɗin.
Cikin ikon Allah tuni aka gano mai wannan kuɗi bayan shekara ɗaya, kuma mai wannan sana’ar ta P.O.S ya kawo miliyan 10 cif ya danƙawa mai ita, inda a take mai kuɗin ya bashi tukuicin dubu ɗari biyar 500k.
Na Allah basa ƙarewa tsawon shekara guda amma yana ta ajiye da miliyan 10 don jiran ko za’a ga mai shi.