E/News

BABBAR MAGANA: Auren Zawarawa Da Aka Yi A Kano Bai Dauru Ba, Domin Babu Sadaki, Inji Hon Garba Yusuf Abubakar

BABBAR MAGANA: Auren Zawarawa Da Aka Yi A Kano Bai Dauru Ba, Domin Babu Sadaki, Inji Hon Garba Yusuf Abubakar

Honarabul Garba ya kara da cewa “Saidai Malamai su taimaka a gyara ko kuma gwamnati ta kawo ciko a baiwa mata sadakinsu.

Yanzu haka a shari’a dubu hamsin ba sadaki ba ne, domin dubu hamsin bai kai sadaki ba”.

Kungiyar Izala Ta Halarci Taron Kaddamar Da Raba Kayan Tallafin Auren Gata (Auren Zawarawa) 1800 A Kano

Kungiyar Izala Ta Kasa Kaskashin Jagorancin Sheikh Dr Abdullahi Balalau Ta Halarci Taron Kaddamar Da Raba Kayan Tallafin Auren Gata (Auren Zawarawa) A Fadar Gwaunatin Jihar Kano.

Taron Wanda Ya Gudana A Yammacin Wannan Rana Ta Asabar Kuma Ya Samu Halartar Shugaban Kungiyar Na Kasa Wanda Babban Sakataren Kungiyar Ya Wakilta Sheikh Dr Kabir Haruna Gombe.

“Tabbas Abinda Gwaunan Jihar Kano Engr Abba Kabir Yusuf Yayi A Yau Na Auren Gata (Auren Zawarawa) A Yau Abune Wanda Allah Yayi Umarni Acikin Al-qur’ani Mai Girma. Muna Yaba Masa Tare Da Addu’ar Fatan Alkhairi Ga Abokan Aikinsa” Inji Sheikh Kabir Gombe.

Allah Ya Sanya Alkhairi Da Albarka A Wannan Aure.

AMEEN.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button