Uncategorized

BIDIYO: Mahaifiyar Haneefa Abubakar Tayi Bayanin Yadda Taji Kan Hukuncin Kisa Da Kotu Ta Yankewa Wanda Ya Kashe Mata Ya

BIDIYO: Mahaifiyar Haneefa Abubakar Tayi Bayanin Yadda Taji Kan Hukuncin Kisa Da Kotu Ta Yankewa Wanda Ya Kashe Mata Ya

Cikin wani bidiyo da akai hira da mahaifiyar haneefa Abubakar wanda malamin makarantar su ya kashe.

Mahaifiyar ta nuna farin cikin ta kan hukuncin da kotu ta zartar na hukuncin kisa akan makashin.

Bayanin da iyayen Hanifa suka yi ga manema labarai bayan alkali a Babbar Kotun Kano ya zartar da hukuncin kisa ta hanyar rataya a kan Abdulmalik Tanko wanda ya kashe dalibar tasa.

Kamar yadda zaku kalli bidiyon bayanin mahaifan Haneefa Abubakar,

A yaune dai Wata babbar kotu a jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta yanke hukuncin kisa kan Abdulmalik Tanko kan samun sa da laifin kashe dalibarsa Hanifa Abubakar.

Mai Shari’a Usman Na’abba da ke jagorantar ƙarar ne ya yanke hukuncin a ranar Alhamis 28 ga watan Yulin 2022.

Ana zargin malaminta Abdulmalik Tanko ne ya sace ta a watan Disambar 2021 tare da kashe yarinyar mai shekara biyar, kana ya binne gawarta a gidansa.

Kisan nata ya ja hankalin duniya inda dubban mutane, ciki har da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, suka yi tur da shi.

Gadai Bidiyon Ku Kalla

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button