Kannywood: An daura Auren Bashir mai Shadda da jaruma Hasana Mohammed

A yau Lahadi, 13 ga watan Maris ne dubban jama’a su ka shaida daurin aure tsakanin babban mai shirya finafinai a masana’antar Kannywood, Abubakar Bashir Maishadda da jaruma, Hassana Mohammed.

Daily Nigerian Hausa ta jiyo cewa, an daura auren a Masallacin Murtala da ke unguwar Hausawa a birnin Kano, kuma ya samu halartar manyan jaruman masana’antar.

Bayan daurin auren, Maishadda ya je shafinsa na Instagram domin nuna godiya ga Allah, inda ya yi hamdallah tare da neman masoya da su taya su da addu’a.

“ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH
“An Daura Aurena Da HASSANA MUHAMMAD. Ina bukatar addu’arku Masoya.”

Wannan aure ya dauki hankali sosai kasancewar yan masana’antar basu cika auren junansu ba.

Gadai Bidiyon Yadda Shagalin Biki Ya Gudana Kusha Kallo Lafiya.

 

Click Here To Drop Your Comment