Uncategorized

BIDIYO: ‘Yan fashi sun gudu da adai daita sahu bayan hallaka matukinsa a Suleja. 8 full.

BIDIYO: ‘Yan fashi sun gudu da adai daita sahu bayan hallaka matukinsa a Suleja. 8 full.

Adai daita sahu
Adai daita sahu

Wasu da ake kyautata zaton ‘yan fashi ne sun hallaka wani matashi mai mai suna Auwalu Muhammad, Dan asalin garin Gumel a jihar Jigawa, tare da guduwa da baburin adai daita sahun da yake Sana’a da shi.

Subscribe our youtube channel for more….

Idris Aliyu(Bilili) wanda shine ubangidan matashin, ya fadawa manaima labarai a Suleja cewa: matashin ya dauki fasinjoji ne zuwa yankin Tapa a jihar Neja.

inda suka shammace shi wajen yi masa mummunan rauni akai da wasu sassan jikinshi tare da janshi zuwa cikin daji su daddaure shi da igiya hadi da kasheshi nan take duk da yunkurin guduwar da yayi domin ya tsira da rayuwarsa.

Har zuwa lokacin kammala hada wannan rohoto dai, rundunar ‘yansandan jihar Neja dai bata ce komai ba game da afkuwar wannan lamari.

Daga:Idris Usman Alhassan Rijiyarlemo

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button