News

Ana Neman Wadanda Suka Cire Kudi da Sahannun Buhari na Bogi, Now 1

Ana Neman Wadanda Suka Cire Kudi da Sahannun Buhari na Bogi

Mai bincike 77 na musamman da Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya nada ya bukaci hukumar yan sanda ta kasa da kasa wato interpol ta sanya ido kan wani ma’aikacin babban bankin Najeriya CBN da wasu mutum biyu.

Matakin ya zo ne bayan bankado wasu takardun bogi da sunan tsohon shugaban Kasar ta Nigeria Muhammadu Buhari na zargin satar dala miliyan shida da dubu dari biyu kafin babban zaben 2023.

Tun farko wani tsohon sakataren gwamnatin Najeriya, Boss Mustapha ya shaida wa babbar kotu a Abuja kamar yadda jaridar DailyTrust ta rawaito cewa takardun da aka yi amfani da su wajen biyan masu sa ido a zaben dala miliyan shida da dubu dari biyu na boge ne.

Read more

Tsohon sakataren gwamnatin Najeriyar ya bayyana haka ne lokacin da ya bayyana a matsayin shaida ta hudu a shari’ar da ake yi kan tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele, bisa zargin karkatar da dala miliyan shida da dubu dari biyu.

Buhari
Buhari

Hukumar EFCC mai yaki da yi wa arzikin kasa ta’annati ta gabatar da karin tuhume-tuhume kan Emefiele da ke da alaka da hada kai wajen aikata laifi da cin amana.

Boss Mustapha ya ce ba shi da masaniya kan abin da ya faru ko da cewa ya bar ofishinsa, inda ya ce ya samu bayani a kai ne a Disamban 2023.

Da aka nuna masa takardar amincewa daga ofishin shugaban kasa, Mustapha ya bayyana cewa takardar ba ta fito daga ofishin shugaban kasa ba kasancewar ya yi aiki tsawon shekara biyar da wata bakwai.

Cikin wata wasika, mai binciken na musamman ya bayyana sunan Odoh Eric Ocheme wanda ma’aikaci ne a CBN da Adamu Abubakar da Imam Abubakar a matsayin sunaye uku da aka aike wa Interpol.

An aike wasikar da aka rubuta ranar 12 ga watan Fabarairu dauke da sa hannun Eloho Okpoziakpo zuwa ga mataimakin babban supeton yan sanda da interpol.

To sai dai rahotanni na cewa mataimakin darekta na sashen ayyuka na babban bankin Najeriya, CBN, Mista Onyeka Ogbu ya shaida wa kotu a ranar Talata cewa tsohon gwamnan babban bankin, Godwin Emefiele ba umarce shi ya fitar da kudin dala miliyan shida da dubu 230 ga wasu masu sanya ido kan zaben, kafin gudanar da wannan zabe.

Visit our Facebook

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button