Kannywood News

Bidiyon Matashiyar Da Tasha Alwashin Cewa Duk Ran Da Tai Ido Biyu Da Adam A. Zango Sai Tayimai Rugumar Da Babu Mai Iya Banbareta Daga Jikinsa

Bidiyon Matashiyar Da Tasha Alwashin Cewa Duk Ran Da Tai Ido Biyu Da Adam A. Zango Sai Tayimai Rugumar Da Babu Mai Iya Banbareta Daga Jikinsa

Wata Matashiya Me suna Giwar Mata wacce ta dade tana bibiyar jarumi adam zango domin tana daya daga cikin manyan masoyan Jarumin, Sai dai Kuma Har Yanzu bata samu damar ganin saba.

Acikin wata Faifan Vedio da jarumi adam Zango ya wallafa a shafinsa na Instagram Wanda har yasa mutane suka ringa zaginsa akan wani masoyinsa daya rugo ya rungume shi, amma ya nuna halin ko in kula Hasali ma ya nuna baiji dadin abinda masoyin nasa yayi mashi ba.

Mutane da dama kowa nata bayyana ra’ayin shi akan wannan alamari daya faru inda wasu ke fadin cewa gaskiya adam Zango bai kyauta ba Kasancewar Ba wani abu bane yasa matashin ya rungume shi illa kawai kauna da yakeyi masa.

https://youtu.be/po7UDegPWnM

Harma wani masoyin Jarumin ya Bayyana cewa abinda jarumin yayi yayi dai dai, domin bai kamata ace ya rungume shi ta baya ba, Kowa akayiwa haka dole yaji haushin abun.

Wasu Kuma sun bayyana cewa Ai dama halin sane, yasha yiwa masoyansa da dama irin hakan don haka ba wani abun mamaki bane ganin hakan daga wurinshi.

Bayan bayyanar bidiyon ne Sai Babbar Masoyiyar Jarumin Wacce ake kira da Giwarmata ta bayyana cewa ita kam duk randa ta hadu da jarumi adam zango to idan ta rungumeshi wlh babu wanda Zai iya banbareta daga jikin shi.

Domin ta dade tana fatan Allah ya hadata da jarumin saboda irin kaunarda take yi masa Amma Har yanzu Allah baisa sun hadu ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button