Kannywood News

Full Bidiyon Yadda Aka Tarbi Murja Ibrahim Kunya Bayan Guduwa Daga Gidan Yari A Kano.

Full Bidiyon Yadda Aka Tarbi Murja Ibrahim Kunya Bayan Guduwa Daga Gidan Yari A Kano.

Murja Ibrahim Kunya
Murja Ibrahim Kunya

Kanawa sun nuna damuwarsu kan sakin Murja Ibrahim Kunya ba tare da bayyana sharuddan belin ta ba

Al’ummar Kano sun nuna damuwarsu kan sakin Murja Ibrahim Kunya daga gidan gyaran hali ba tare da bayyana wa jama’a sharudan belin ta ba.

Jami’an hukumar Hisba ta jihar Kano sun kama shahararriyar TikToker ne biyo bayan zargin ta da yada wasu munanan bidiyo a dandalinta na sada zumunta .

Murja Ibrahim Kunya
Murja Ibrahim Kunya

lamarin da ya saba wa tanadin tsarin shari’ar Musulunci na jihar Kano a shekarar 2000.

Kakakin hukumar Hisbah ta Kano, Malam Lawal Ibrahim Fagge, ya shaida wa manema labarai cewa an kama Kunya ne bayan da makwabtan ta suka kai karar ta kan tallata lalata da TikToker ke yi a cikin al’umma.

Daga baya kotun shari’a ta jihar Kano karkashin jagorancin Malam Nura Yusuf Ahmed ta bayar da umarnin tsare ta na tsawon mako guda a gidan gyaran hali amma daga baya aka sake ta ba tare da bayyana sharudan sakin ta ba.

Wannan lamarin ya janyo cece-kuce a jihar Kano.

Gidan gyaran hali na Nijeriya reshen Jihar Kano ya tabbatar da cewa tun ranar Alhamis ɗin da ta gabata ya saki Murja Ibrahim Kunya daga gidan bayan samun takardar daga kotu.

Mai magana da yawun gidan gyaran halin SC Musbahu Lawan Kofar Nasarawa ya tabbatar wa TRT Afrika cewa sai da suka samu takarda daga kotu tukuna suka sake ta.

Kokarin samun bayanai daga Muzammil Ado Fagge jami’in hulda da jama’a na Kotun Shari’ar Musulunci ta Jihar Kano dangane da sharuɗɗan belin ko kuma dakatar da shari’ar ya ci tura domin bai amsa kiran da wakilin jaridar Justice Watch News ya yi masa ba.

Barista MM Isa, wani lauya a Kano, ya jaddada cewa ikon bayar da belin yana hannun kotu, yana mai jaddada wajabcin yin amfani da wannan iko cikin adalci, musamman a lokuta da laifin da ake zargin zai iya yin illa ga al’umma.

KU KALLI CIKAKKEN BIDIYON ANAN…👇👇👇👇👇

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button