Kannywood News

Hotuna na da Aisha Humaira ba na aure ba ne, na talla ne munyi ne dan kawai mu– Mai-shadda

Hotuna na da Aisha Humaira ba na aure ba ne, na talla ne — Mai-shadda

Fitaccen Mai tsara fina-finan Hausa na Kannywood, Abba Bashir, wanda a ka fi sani da Mai-shadda ya musanta rahotannin da ke yawo a kafafen sadarwa cewa zai auri jaruma Aisha Ahmad, wacce a ka fi sani da Aisha Humaira.

A yau Alhamis ne dai Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa Mai-shadda na daf da angwance wa da Aisha Humaira, bayan da ya wallafa hotunan da su ka ɗauka tare a shafinsa na Instagram.

“Zan yi wuff da gishiri ambassador.”, haka Mai-shadda ya rubuta a saman hotunan da ya wallafa a Instagram ɗin.

Bayan wallafar da ya yi, jaruma Aishat Humaira ta sake wallafa hotunan a shafinta na Instagram, inda ta haɗa da alamar soyaiya.

Hakan ne ya sanya a ka dinga yayata wa cewa aure jaruman na Kannywood za su yi.

Sai dai kuma wata majiya da ke kusa da Mai-shadda, a yammacin Alhamis ta shaida wa Daily Nigerian Hausa cewa hotunan ba na aure ba ne, na talla ne.

A cewar majiyar, jaruman biyu sun ɗauki hotunan ne domin yi wa Kamfanin Shehu Danƙwarai da ke kasuwar Kantin Kwari.

Majiyar ta ce nan ba da daɗewa ba Mai-shadda zai wallafa tallan a shafinsa na Instagram.

“in an jima kaɗan ma zai saki tallan a kan Instagram ɗin shi sabo da mutane su na ta damun shi da waya.

“Tallan Kamfanin Shehu Danƙwarai ne, in an jima zai sanya shi a Instagram,” in ji majiyar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button