Kannywood News

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raju’un A Karshe Dai Allah Ya Amshi Ran Jarumin Fim Garba SK

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raju’un A Karshe Dai Allah Ya Amshi Ran Jarumin Fim Garba SK

Allah Ya yi wa fitaccen ɗan wasan fina-finan Hausa Sani Garba SK rasuwa a yau Laraba a birnin Kano, bayan ya sha fama da rashin lafiya.

Wani fitaccen furodusa Abdul M Amart Mai Kwashewa ne ya tabbatar wa da BBC rasuwar ɗan wasan.

Marigayin ya rasu ne a Asibitin Muhammadu Abdullahi Wase da ke Nasarawa a ranar Laraba da yamma.

“Sani SK ya kai kusan shekara uku yana jinya a tsattsaye, amma rashin lafiyar ta taso masa sosai ne a baya-bayan inda ya shafe mako biyar yana jinya a asibitin,” in ji Amart.

Amart ya ƙara da cewa tun asali cutar ciwon suga ce yake fama da ita, wacce daga bisani ta haifar masa da cututtuka irinsu ƙoda da hanta da hawan jini.

A baya dai an sha yaɗa jita-jitar rasuwar Sani SK, inda ya dinga musantawa da kansa ma a wasu lokutan.

“A ranar yau da ya rasu ɗinnan aka fara yi masa wankin ƙoda,” a cewar Furodusa Amart, wanda shi ke tsaye a kan kula ɗaukar nauyin kula da lafiyar marigayin.

Sani Garba SK ɗan asalin unguwar Zage ne a cikin birnin Kano, kuma a baya kafin ya fara harkar fina-finai mai yabon Manzon Allah ne a ƙungiyar Usha’un Nabiyyu.

Kafin kwanciyarsa a Asibitin Nasarawa sai da ya kwanta a Asibitin Murtala da ke cikin birni.

Abdul Amart ya ce tuni aka tafi da gawar mamacin gida, kuma za a yi jana’izarsa a gobe Alhamis.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button