Kannywood News

Masha Allah: Tijjani Gandu Lafiya Ta Fara Samuwa

Bayan tsautsayin hadarin mota dayayi Mawakin Siyasarnan na Kano Tijjani Gandu, ya fara Samun sauki cikin yardar Allah.

A Cikin wata ziyara da jarumin masana’antar fina finan Hausa ta Kannywood yakai masa wato Abba El’Mustapha, Wanda Akafi sani da Abba Na Abba Ya kaimasa ziyara a gidansa.

Duba da yadda Jama’a Suka damu ainun na rashin lafiyar Mawakin yasa muka tuntubi na jikin Mawakin, Inda ya baiyana mana cewa.

” Ayanzu haka Tijjani na Samun sauki Kuma yana nan Yana shirin fitar da wakar Rantsuwa da Za’ayi 29 ga wannan watan.

Ya Kuma Yi godiya ga Al’umma bisa adduo’insu ga Mawakin fatan Allah ya Tashi Kafadu yasa kaffarane.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button