Uncategorized

Tirqashi: Abba Ya Fara Rusau A Kano Kan Gine Ginen Da Akayi A Filayen Gwamnati Da Ganduje Siyar

Tirqashi: Lallai Abba Bada Wasa Yazo Ba, Ku Kalli Yadda Ya Fara Da Rusau A Jahar Kano

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusif ya jagoranci rushe wasu gine gine a kewayen filin sukuwa dake unguwar Nassarawa a daren jiya Juma’a, wadanda aka yi lokacin Tsohuwar gwamnati.

Yayin aikin rusau din Gwamnan na tare da rakiyar kwamishinan yan Sandan Kano CP Muhammad Gumel da manyan jami’an gwamnati da kuma tarin jami’an tsaro.

Jim Kadan Da Kammala Rusau Din Matasa Suka Shiga Cin Ganima A Wajen.

Mutane fa sai anayi musu tamsiri suke gane abubuwa sosai. Tun a jawabin rantsuwa ranar May 29, Balaraben Gwamna Abba ya soke duk wani gini da akayi a filayen gwamnati ba bisa kaida ba. Ya kuma bawa jamian tsaro ikon kula da su. Idan kana jira har yanzu sai kaga notice daga KNUPDA kafin kasan Annabi ya faku, zaka wayi gari da sakamakon bulldozer a gininka.

Salin alin ka lallaba kaje ka cire abinda ke da amfani kafin a iso kanka. New sheriff ne ke sanar da sabon salo yazo. Gyaran karaya dama haka yake: sai an ji radadi sannan sauki ya samu.

Abi doka a zauna lafiya. Greed ne ya sa mutane suka rika zuba kudinsu a harkalla da hadadar Gandollar. Ga irinta nan!

Ra’ayin Musa Ibrahim Wanda Ya Wallafa A Shafin Sa Na Sada Zumuntar Facebook.

Ku Kalli Bidiyon Anan 👇👇👇👇

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button