Kannywood News

Yadda Ƴan Bindiga Sun Haddasa Mummunan Hadari A Hanyar Katsina Zuwa Jibia Tare Da Kwashe Matafiya

Yadda Ƴan Bindiga Sun Haddasa Mummunan Hadari A Hanyar Katsina Zuwa Jibia Tare Da Kwashe Matafiya

A yammacin jiya Laraba ne ‘yan bindiga suka ƙara saka shinge akan babban titin Jibia zuwa Katsina a tsakanin garin Kadobe da Farun Bala.

Daya daga cikin waɗanda abin ya ritsa da su ya tabbatar mana cewar “Muna cikin tafiya sai muka yi karo da su yayin da suka harbi tayar motar da muke ciki.

Wanda hakan ya yi silar kwacewar motar daga hannun Direbanmu ta sauka ƙasa, sannan suka ci gaba da harbin kan Mai uwa da wabi, yayin da suka kashe wani fasinja har Lahira sannan suka raunata wasu”

Daga karshe kuma “an ta’addar sukayi awon gaba da wasu daga cikin Fasinjojin amma cikin ikon Allah Jami’an tsaro sun kai ɗauki, wasu a cikin motar APC (wato Bullet Proof), wasu a cikin mota kirar Koker yayin da wasu suke a jirgin sama. kuma sun samu nasarar kutsawa tare da bibiyarsu har cikin dajin.

A kwanakin nan dai saka Shinge a hanyar ta Jibia ya zama ruwan dare yayin da lokata da dama kawai sai kaji ance an tarbe hanyar da rana kata, akwai wani ma Ɗan Ta’adar da ake mashi laƙabi da Solar ma’ana dai shi da rana yake fitowa kata ya aikata ɓarnar shi yayi gaba abinshi.

Muna addu’ar Allah ya kawo mana ƙarshen wannan Ibtila’in ya zaunar da ƙasar mu lafiya Amin.

Daga Muhammad Aminu Kabir

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button