News

Ƴan ta’adda sun kashe mutum 1 sun kuma hana jirgi tashi a filin jirgin saman Kaduna

Ƴan ta’adda sun kashe mutum 1 sun kuma hana jirgi tashi a filin jirgin saman Kaduna

A yau Asabar ne dai wasu da a ke zargin ƴan ta’adda ne su ka dira a filin tashi da saukar jiragen sama, inda su ka hana jirgi tashi.

Jaridar Nigerian Tribune ta rawaito cewa jirgin, wanda a ka tsara zai tashi zuwa Jihar Legas da misalin ƙarfe 12:30 na rana, bai iya tashin ba saboda yan ta’addan, ɗauke da muggan makamai, sun mamaye filin titin jirgin.

Jaridar ta jiyo cewa ma’aikata da fasinjoji sun ranta a na kare domin tsira da ransu lokacin da ƴan ta’addan su ka shiga filin titin jirgin.

Rahotanni sun baiyana cewa ƴan ta’addan sun lashe wani maaikacin Hukumar kula da Sararin saman Nijeriya, NAMA.

Sai dai kuma, a cewar Nigerian Tribune an kawo sojoji filin jirgin saman domin samar da tsaro.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button