News

MASHA ALLAH: Bidiyon Yadda Gidauniyar FASAUDAT Ta Tallafawa Fatima Wadda Ta Samu Kaddarar Datsewar Kafa

MASHA ALLAH: Bidiyon Yadda Gidauniyar FASAUDAT Ta Tallafawa Fatima Wadda Ta Samu Kaddarar Datsewar Kafa

Wata Gidauniya Mai Suna Gidauniyar FASAUDAT Ta Tallafawa Fatima Wadda Ta Samu Kaddarar Datsewar Kafa Asanidiyar Tukin Gangaci.

Da Wani Matashi Yayi A Ranar Da Suke Murnar Kammala Jarabawar Fita Daga Makarantar Wato Jarabar Neco.

Gidauniyar Fasaudat Support Foundation ta tallafawa yarinyar nan mai suna Fatima da ta rasa kafarta sanadiyar tukin Ganganci da wani yaro yayi.

Shugabar Gidauniyar Hajiya Fatima Ahmad Maigari tareda sauran jagororin gidauniyar ne suka ziyarci Fatima.

A asibitin koyarwa ta jam’iyar Danfodio wato UDUTH Inda Take Amsar Jinya Karkashin Kulawar Likitocin Kashi.

Hajiya Fatima Maigari ta nuna kaduwa da halin da Fatima ta sami kanta inda ta Shawarci Fatima ta daukeshi a matsayin kaddara daga Allah.

 

Fatima Maigari ta bayarda tallafin kudi da wasu kayyaki ga fatima A Matsayin Goran Dubiya.

Daga Karshe An gudanar da adduo’in samun lafiya ga Fatima Tare Da Addu’ar Allah Ya Kiyaye Gaba Amin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button