Kannywood News

Abin Da Ya sa Arewa24 Suka Canza Salma Daga Kwana Casa’in

‘Abin Da Ya sa Arewa24 Suka Canza Salma Daga Kwana Casa’in’

Salisu T. Balarabe, Shine daraktan shirin Kwana Casa’in, ya bayyana dalilin Da Yasa Aka sauya tauraruwar da ke taka rawa a matsayin Salma.

A wata hira da Yai Da BBC Hausa, daraktan ya Bayyana cewa ita da kanta ce ta bayyana Musu cewa ba za ta ci gaba da fitowa a shirin ba.

A cewarsa: “A tsarinmu na Kwana Casa’in duk lokacin da za a gabatar da wani zango, akan tuntubi jarumai kafin lokaci cewa an sa lokacin da za a dauki wannan zangon; wadansu sukan fadi cewa ba za su samu yi ba saboda yanayi na karatu ko kuma wani dalili da su suka bar wa kansu sani.

Lokacin da muka tuntubi ita Salma a kan cewa za mu dauki shirin Kwana Casa’in Zango na shida ta fada mana cewa gaskiya ba za ta samu dama ba, mun so mu san dalili sai ta fada mana cewa yana da nasaba da iyayenta wanda ba lallai ne ta iya bayyanawa b.”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button