Kannywood News

Abinda Yasa Firodusa Abubakar Mai Shadda Zai Aure Jaruma Aisha Humaira

Mai-shadda na shirin angwance wa da Aisha Humaira

Alamu sun nuna cewa, fitaccen Mai haɗa fina-finan Hausa na Kannywood, Abba Bashir Mai-shadda zai aure ɗaya da ga cikin taurarin masana’antar, wato Aisha Ahmad, wacce a ka fi sani da Aisha Humaira.

Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa an fara rade-radin cewa Mai-shadda zai angwance a watan Maris, sai dai kuma ba a bayyana wacece amaryar ba.

Kwatsam, sai ga Mai-shadda ya je shafinsa na Instagram inda ya sanar da cewa zai yi wuf da jakadiyar gishirin Dangote tare da saka hotunansu na kafin aure.

A safiyar Alhamis ne a ka wayi gari da ganin sabbin kyawawan hotunan kafin aure na fitaccaen mai haɗa fina-finan Hausa ɗin da jaruma Aishatul Humaira.
Tun farko dai, shafin Labaran.

Haka shima shafin labaran Kannywood a Twitter, a kwanaki biyu da suka gabata, ya bayyana cewa Mai-shadda zai angwance a cikin watan Maris mai kamawa, sai dai ba a san wacece amaryar ba.

Kwatsam babu zato ba tsammani, sai ga shi da kansa ya wallafa hotunansa tare da jaruma Aisha Humaira, inda ya bayyana cewa auren ta zai yi.

Kamar yadda wallafar tace: “Zan yi wuff da gishiri ambassador.”

Bayan wallafar da ya yi, jaruma Aishat Humaira ta sake wallafa hotunan a shafinta na Instagram, inda ta haɗa da alamar soyaiya.

Sai dai ko bayan bayyanar hotunan, babu takamaiman lokacin auren na jaruman Kannywood.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button