News

An Cika Hannu Da Wani Gardi Mai Amfani Da Sunan Layla Ali Othman Yana Damfarar Jama’a Kudi

An Cika Hannu Da Wani Gardi Mai Amfani Da Sunan Layla Ali Othman Yana Damfarar Jama’a Kudi.

 

An kama wani matashi mai suna Umar Gambo kuma an tuhume shi da laifin damfara ta internet da yin sojan gona. An zarge shi da yin sojan gona yana cewa shi ne Layla Ali Othman, yana tambayar mutane su aika masa da kudi ta hanyar aika hotunan wadda yake karya da sunanta.

Sati biyu da ya wuce, Umar Gambo ya tuntubi wani abokin Layla ya nemi ya aika masa kudi da sunan za a yi aikin taimako da su wanda kuma karya ce da yake yi da sunan Layla.

Ya nemi ya ba shi 500,000 kuma har da tura masa lambar account domin ya sa kudin. Daga nan aka rika bin diddigin Umar aka kuma kama shi.

An gabatar da shi gaban kotu magistrate da ke Abuja a yau, an kuma bayar da belinsa kan kudi N200k kuma an nemi ya kawo wanda zai tsaya masa.

Amma a yanzu, yana tsare a gidan yari har sai ya cika sharudan beli da kotu ta saka… An daga shari’ar Wannan ya zama gargadi ga duk wanda yake damfarar mutanen ta intanet.. ka sani Rana dubu ta barawo, rana daya ta mai kaya.

Laiyla ta ce “Kusani
@hajiyalaila….
@hajiyalaila… da sauransu account din macuta ne… da kun ga haka ku taimaka ku shigar da korafi a kansu, mu rika kiyayewa da masu damfara ta internet Ku sani cewa Layla Ali Othman ba ta wani kasuwanci online, ba kuma ta tambayar kowa kudin gudanar da ayyukan taimakon alumma. Mun gode”.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button