News

Ana kuka har da hawaye A kan 5K din da muke rabawa mutane duk wata, saboda jin dadi – Sadiya

Ana kuka da hawaye kan 5K din da muke bayardawa duk wata, saboda jin dadi – Sadiya

Ministar Sadiya Umar Farouq, ta ce tallafin da ake bayarwa na Naira 5,000 a duk wata yana da matukar muhimmanci ga ‘yan Najeriya masu rauni.

Ministan ta bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin ganawa da manema labarai na fadar gwamnati.

Ta yi wannan tsokaci ne a lokacin da aka tambaye ta game da cigaban da aka samu na shirin gwamnatin tarayya na ceto ‘yan Najeriya miliyan 100 daga matsanancin talauci.

DAILY TRUE HAUSA – Minstar ta ce, “Idan ka duba mutanen da suke karbar, Naira 5,000 suna amfanuwa sosai a gare su, domin wadannan na canza rayuwar marasa galihu da canza musu matsayi, amma ni da kai Naira 5,000 ma ba ta isa mu sayi katin kira na waya ba, wannan shi ne bambancin”.

“Idan mutane suka ce Naira 5000 ba ta taimakawa mutane, wannan magana ce ta ba dai-dai ba, mun ga wadannan mutanen da aka ba su wannan N5,000 suna yin kuka suna zubar da hawaye, domin ba su taba ganin Naira 5,000 a rayuwarsu ba”. Inji ta

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button