News

AYIRIRI: Mai Martaba Sarkin Daura Ya Sake Yin Wuff Da Budurwa Danya Sharaf Mai Shekaru 22, hotuna Sun Bayyana.

Ayiriri: Sarkin Daura Ya Sake Yin Wuff Da Budurwa Danya Sharaf Mai Shekaru 22, hotuna Sun Bayyana.

Kamar Yadda Shafin Labarai Na HausaLegitNg Suka Rawaito Cewa.

Mai Martaba Sarkin Daura, Alhaji Dr Umar Faruk mai shekaru 91 ya kara yin wuff da budurwa danya shakaf mai shekaru 22.

Inda Suka Kara Da Cewa An daura auren ne ba tare da wasu manyan shagulgula ba a makon da ya gabata,

Tuni dai amarya Aisha Gona Safana ta tare a dakinta inda ta tabbata sabuwar gimbiya kuma amaryar tsohon basaraken.

Wannan labarin ya dauki hankali sosai a shafin sada zumunta, yayinda jama’a suka dinga yiwa sarkin fatan Alkhairi.

Ita amarya tasha Addu’a tare da fatan Alkhairi a dandalin sada zumunta

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button