Ƴan Sanda a Kano sun kama matashin da ya jefa tsohuwa mai shekara 80 a rijiya ta rasu

Yan sanda a Jihar Kano sun cafke wani matashi mai suna Naziru Magaji, ɗan shekara 25 da a ke zargi da kashe wata tsohuwa mai kimanin shekara 80 a duniya, ta hanyar jefa ta a rijiya bayan ya lakaɗa mata duka.

Ana zargin Magaji, mazaunin ƙauyen Kununu, Yalwa Danziyal da ke Ƙaramar Hukumar Rimin Gado a Jihar da yin aika-aikar-aikat a kan tshohuwar mai suna Habiba Abubakar, bayan ya yi mankas da kayan maye.

Kakakin Rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya tabbatar da kama matashin a cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Juma’a.

A cewarsa, “Da misalin karfe 1:30 na ranar Alhamis, 24 ga watan Maris, 2022, mun samu korafi daga wani mazaunin ƙauyen Wangara da ke Karamar Hukumar Tofa a Jihar Kano cewa da misalin karfe 12:00 na ranar, wani matashi mai kimanin shekara 25 mazaunin kauyen Kununu Yalwan Danziyal a Karamar Hukumar Rimin Gado da ke Kano, ya lakada wa yayarsa, Habiba Abubakar, mai kimanin shekara 80 duka, sannan ya jefa ta a rijiya.

“Da samun labarin, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano, Sama’ila Shuaibu Dikko, ya umarci jami’ai karkashin jagorancin CSP Isyaku Mustapha da kuma Baturen ’Yan Sanda na Tofa su je wajen.

“Da zuwansu suka ciro tsohuwar daga rijiyar, sannan suka garzaya da ita Babban Asibitin garin Tofa, inda likitoci suka duba ta, sannan suka tabbatar da cewa ta rasu.

“Binciken farko-farko ya nuna mana wanda ake zargin ya ce yana da tabin hankali, kuma sai da ya yi mankas da kayan maye kafin ya aikata danyen aikin,” inji sanarwar.

Kakakin ya kuma ce tuni Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar ya ba da umarnin mayar da lamarin ga Sashen Binciken Manyan Laifuffuka na Rundunar.

Ya ce da zarar sashen ya kammala bincikensa za a gurfanar da wanda ake zargin gaban kotu don ya girbi abin da ya shuka.

Ga Full Bidiyon Yaron Ku Kalla

Click Here To Drop Your Comment