News

BIDIYO: Abin Tausayi Tsohuwa Ta Fashe Da Kuka Bayan Da Aka Kwace Filin Da Ta Siya Da Kudin Ta

Abin Tausayi Wata Tsohuwa Ta Fashe Da Kuka Bayan Da Aka Kwace Filin Da Ta Siya Da Kudin Ta.

Wata Tsohuwa Mai Shekaru Da Yawa, Ta Fashe Da Kuka A Tsakiyar Wani Fili.

Inda Take Ta Kaiwa Allah Karar Cewa Wasu Masu Kudi Sun Kwace Mata Filin Da Ta Siya Da Kudin Ta Zata Ginawa Marayu.

Kamar Yadda Zaku Gani A Cikin Wannan Bidiyon, Tsohuwar Tace Masu Kudi Ne Suke Neman Yi Musu Karfa Karfa Akan Filin.

Bidiyon Da Ya Karade Shafukan Sada Zumunta, Wanda Fitacciyar Marubuciyar Nan Wato Fauziyya D. sulaiman Ta Wallafa.

Inda Ta Rubuta Cewa.
INNALILLAHI WA’INNA ILAIHI RAJIUN 😭😭😭

Allah ka kawowa wannan baiwar taka dauki, duk da ban Santa ba na ji tausayinta matuka, ta tara da kwabo da taro ta sayi fili domin ginawa ta zauna da marayunta ana neman a kwace.

Jama’a Da Dama Sun Waallafa Bidiyon Tare Da Neman Hukuma Ta Shiga Maganar Domin A Kwatowa Wannan Tsohuwa Hakkin Ta.

Ciki Kuwa Hadda Baxallah Germany Sarkin Bai, Wanda Shima Ya Wallafa A Shafinsa Kamar Haka.

INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI’UN… 😢😢😢

Wasu azzalumai suna yunkurin kwacewa marayu filaye, a garin TSAMIYA BABBA BAKIN GADA dake jihar Kano…

Allah kar ka bari a azzalumai suci nasara akan wadannan marayun. Albarkacin annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ya Allah. 🤲🤲😭😭😭😭😭😭

Gadai Bidiyon Ku Kalla

https://youtu.be/Zby35DBH3vI

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button