Uncategorized

BIDIYO: Allah Sarki Mahaifin Ummi Matar Aure Mai Dauke Da Ciki Wadda Aka Shiga Har Gidanta Aka Kashe Ta A Jigawa

BIDIYO: Allah Sarki Mahaifin Ummi Matar Aure Mai Dauke Da Ciki Wadda Aka Kashe Ta A Jigawa

Yadda na ji da kashe ‘yata mai ciki a gidanta da ke Jigawa’

Mutane na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu kan rahoton mutuwar Ummi Garba, wata matar aure mai ciki da aka kashe a gidanta da ke ƙaramar hukumar Haɗeja a jihar Jigawa da ke arewacin Najeriya.

Masu amfani da kafafen sa da zumunta sun nuna kaɗuwa da takaicin wannan kisa da aka yi wa matar auren.

Mahaifinta da ake kira Malam Garba Umar ya shaida wa BBC cewa wasu mutane ne suka shiga gidanta suka kashe ta.

A tattaunawar tasa da BBC, mahaifin Ummi ya ce ganin da ya mata na ƙarshe shi ne a ranar Lahadi lokacin da ta je bikin ƙanwarta gida.

“Ummi ta zo gida a ranar Lahadi kuma tare muka wuni saboda ana bikin ƴar uwarta, kafin daga bisani mijinta ya zo ya ɗauke ta suka tafi, shi ne ganin da ya yi wa ƴar tasa na ƙarshe.”

“Ɗan uwana ne ya kira ni a waya ranar Laraba ya shaida mini cewa wasu mutane sun kashe Ummi, nan da nan na tafi gidanta, abin da idona ya gani na takaici ne kuma ba zan taɓa mantawa da hakan ba.”

Malam Garba ya ce a kan idonsa aka fitar da gawar Ummi a gidan da take zaune da mijin da ta aura wata 19 da suka gabata.

Ya tabbatar da cewa ‘yar tasa na ɗauke da ciki kamar yadda ma’abota shafukan sa da zumunta ke ta faɗa a shafukansu.

“Eh tana da juna biyu kuma tana zuwa awo, cikin shi ne na biyu bayan na farkon da ta samu wanda aka yi barin shi bayan wani lokaci.”

Ya ce ƴar tasa mai shekara 26 tana da biyayya kuma ba zai taba mantawa da ita ba.

A ƙarshe ya ce fatan cewa hukumomi za su yi abin da ya dace wajen gano wadanda suka yi wa ‘yar tasa kisan gilla.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button