Uncategorized

BIDIYO: An Gano Wani Gida Da Ake Ginin Sa Da Takardun Al’qurani Ake Zuba Lintarsa Da Alluna A Jahar Kano

BIDIYO: An Gano Wani Gida Da Ake Ginin Sa Da Takardun Al’qurani Ake Zuba Lintarsa Da Alluna A Jahar Kano

Wani rahoto da muke samu daga jahar kano, na cewa an gano wani gida da ake ginawa da Alqur’ani mai mai girma.

Kamar yadda zaku kalli bidiyon wannan gida a kasa, mutanen unguwar ne suka fara ankarewa cewa kamar akwai lauje cikin nadi ta yadda ake gina wannan gida.

Inda suka zuba idanu sai suka fahimci cewa ana cusa wasu takardu acikin ramukan bulo din da aka dora ginin gidan.

Da suka bi diddigi suka tsanan ta binciken kwakwaf sai suka tarar ashe takardun Alqur’ani mai girma ne.

Sannan sannan a fili din gidan sai akai amfani da Alluna wajen zuba lintar gidan kamar yadda gidan radio Dala FM kano ya rawaito.

Al’ummar wannan yanki sunyi kira ga hukumar hisbah da tazo ta dauki mataki tunkan yan unguwa su dauki doka a hannu.

Gadai Rahoton Ginin Wannan Gida

https://youtu.be/oEYvl-gyCgc

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button