SUBHANALLAH: Bidiyon Yadda Aka Kekketa Kur’ani Ana Cusawa A Cikin Ginin Wani Gida A Kano Sannan Aka Zuba Lintar Gidan Da Alluna.

A jihar Kano al’umma sun gano wani gida da ake ginawa a Unguwar Damfami ta yankin ƙaramar hukumar Kumbotso, wanda ake zargin ana cusa takardaun Al-Qur’ani da Alluna da rubutu ana gine su a ginin gidan.

Kazalika, Al’ummar wannan yankin, sun yi ƙorafi kan ba za su bari a ci gaba da irin wannan ginin a cikin yankin su, Hakan tasa tuni suka rushe ginin tare da miƙa mai gidan hannun hukuma.

Kamar yadda zaku kalli bidiyon a kasa, dafara dai mutanen unguwar ne suka fahimci cewa kamar akwai rashin gaskiya game da yadda ake gina gidan.

Inda suka zuba idanu sai suka fahimci cewa ana cusa wasu takardu acikin ramukan bulo din da aka dora ginin gidan.

Da suka bi diddigi suka tsanan ta binciken kwakwaf sai suka tarar ashe takardun Alqur’ani mai girma ne.

Allah Ta’ala mun tuba ka yafe mana karka kama mu da laifin wasu daga cikim wawayen cikin mu.

Gadai bidiyon ku kalla

Click Here To Drop Your Comment