News

BIDIYO: An kama sojan da ya kashe farar hula 7 a Borno, in ji Rundunar Sojin Ƙasa

An kama sojan da ya kashe farar hula 7 a Borno, in ji Rundunar Sojin Ƙasa

Rundunar Sojin Ƙasa a yau Juma’a ta tabbatar da kama wani soja da a ke zargin sa da kashe farar hula bakwai, da su ka haɗa da wata yarinya ƴar shekara 3 a Ƙaramar Hukumar Mafa a Jihar Borno.

Jami’in Gudanar da Binciken Sirri na Rundunar ‘Operation Hadin Kai’, Obinna Azuikpe ne ya baiyana haka a taron manema labarai kan aikace-aikacen sojoji a Arewa-maso-Gabas.

Azuikpe ya ƙara da cewa mutane 16 sun ji raunuka daban-daban a yayin harbin da sojan ya yi, wanda ya faru a ranar Talata a kasuwar Mafa.

Ya ce tuni a ka garzaya da wadanda su ka samu raunukan, inda shi kuma sojan da ya yi harbin tuni ya shiga hannun ƴan sanda.

Ya ce an kuma samun wasu lamura guda biyu inda ƴan sanda su ka hare sojoji a Maiduguri, inda ya danganta hakan da tunzuri da kuma shan kwayoyi.

GA CIKAKKEN BAYANIN NAN KU SAURARA

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button