News

BIDIYO: An kubutar da mahajjatan jihar Sokoto daga harin ‘yan bindiga

An kubutar da mahajjatan jihar Sokoto daga harin ‘yan bindiga

Gwamnatin jihar Sokoto da ke arewacin Najeriya ta tabbatar da kai hari kan jerin motocin maniyyata aikin Hajji da suka fito daga karamar hukumar Isa.

Maniyyatan suna kan hanyarsu ne ta zuwa garin Sokoto, babban birnin jihar domin tashi zuwa kasar Saudiyya, a lokacin wasu da ake zargin barayin daji ne suka auka wa ayarin motocinsu.

Sai dai sanarwar da gwamnatin Sokoton ta fitar ta ce maniyyatan sun isa garin Sokoto lafiya tare da rakiyar jami’an tsaro.

A cewar Kamishinan Sadarwa, Isah Bajini Galadanchi, tuni an ci gaba da shirye-shiryen kwashe maniyyata aikin Hajjin zuwa kasa mai tsalki ba tare da wata matsala ba.

Dama yankin Isa da ke Gabashin Sokoton na daga cikin wuraren da yan fashin daji ke kai hare-hare sosai a Arewacin Najeriya.

A nan ne watannin da suka gabata ake zargin yan fashin dajin sun kone motar fasinja dauke da mata da kananan yara, yayin da suke kokarin ficewa daga yankin don tsere wa rikici.

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button